Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Jaridar “Annashrah” ta kasar Lebanon ta nakalto Sheikh Ahmad Qattan shugaban kungiyat “Qauluna Walfilu” yana fadar haka a wani jawabi da ya gabatar a yau Asabar, ya kuma kara da cewa gwamnatin kasar Amurka ba za ta yiwa mutanen kasar Lebanon kome ba sai kokarin kaskantasu.
Sheikh Qattan ya yi kira ga yan siyasa da kuma mutanen kasar Lebanon wadanda suke bin Amurka sauka da kafa kan cewa su dauki darasi kan abinda ya faru da mutanen Afganistan.
Dangane da zancen wasu ‘yan kasar na cewa kungiyar Huzbullah tana shishigi cikin ayyukan gwamnatin kasar wadanan sun bayyana haka ne don biyan bukatunsu kawai ba don neman alkhairi ga muaten kasar ba.
Kasar Lebanon dai ta fada cikin halin kaka-ni-kayi na rigingimun siyasa da kuma tabarbarewar tattalin arzikin kasar tun fiye da shekaru biyu da suka gabata.
A ranar Alhamis da ta gabata, kuma ranar Ashura ne, shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar ya bada sanarwan cewa jirgin daukar makamshi zai tashi daga kasar Iran zuwa kasar ta Lebanon.
Kuma ya gargadi Amuka da Isar’ila kan cewa duk wanda ya taba jirgin kamar ya taba kasar Lebanon ne.
342/